4 Nuwamba 2020 - 10:47
Sarkin Qatar Ya Jaddada Bukatar Kafa Kasar Falasdinu Mai Zaman Kanta

Sarkin kasar Qatar Tamim bin Hamd ya sake jaddada matsayin gwamnatin kasar na tallafawa al-ummar Falasdinu har zuwa lokacinda za’a kafa ‘yentacciyar kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Aljazeerah ta kasar Qatar ta nakalto sarki Tamim ya na fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa za’a kafa kasar Falasdinu ko badade ko ba jima a kasar Falasdinu, kuma mai babban birni a birnin Qudus mai alfarma.

A wani labarin kuma shugaban majalisar dokokin kasar ta Qatar Ahmad bin Abdullahi ya bayyana ‘yencin fadin albarkanin baki wanda gwamnatin kasar Faransa take goyon bayan, a matsayin abin takaici, don suna hada har da wulakanta wadanda wasu addinai suke girmamasu ba.

A cikin watan da ya gabata ne shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana goyon bayansa ga wata jarida mai suna Chali Eddo wacce ta buga zane-zanen batancin ga manzon All.. (s), wanda ya ta da hankalin musulmi da dama a duniya.

342/